Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sudan ya bukaci kwamitin tsaron MDD ya waiwayi takunkumin yankin Darfur
2019-12-13 10:16:49        cri
Jakadan kasar Sudan a MDD Omer Mohamed Ahmed Siddig, ya bukaci kwamitin tsaron majalisar, da ya yi duba kan yiwuwar janye takunkumin da aka kakabawa yankin Darfur.

Jakadan ya ce, yanayin da ya sabbaba shigar da dakarun gwamnatin Sudan dake yankin Darfur cikin takunkumin a shekarar 2005 a yanzu ya sauya, kuma Sudan din da aka sani a baya a yanzu ta sauya salo. Kazalika rahotanni da dama da aka wallafa game da yanayin Darfur na nuna cewa, babu sauran bukatar ci gaba da aiwatar da wani takunkumi a yankin.

Bugu da kari, a cewar jami'in, gwamnatin Sudan mai ci ta riga ta ayyana tabatattun matakan dakatar da bude wuta a dukkanin sassan kasar, ta kuma fara aiwatar da shawarwarin wanzar da zaman lafiya tsakaninta da kungiyoyi masu dauke da makamai.

Daga nan sai ya bayyana fatan ganin dorewar tattaunawa tsakanin tsagin gwamnatin Sudan, da bangaren 'yan tawaye a birnin Juba, fadar mulkin kasar Sudan ta kudu, matakin da zai share fagen cimma cikakkiyar yarjejeniya, wadda za ta kai ga cimma zaman lafiya da daidaito a Sudan.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China