Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta kudu ta kaddamar da sabuwar tashar wutar lantarki mai karfin MW100
2019-11-22 11:44:17        cri
Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kirr, ya kaddamar da sabuwar tashar wutar lantarki mai karfin MW100, wadda kashin farko na aikinta zai samar da lantarki ga birnin Juba da yankunan dake kewaye da shi.

Salva Kirr, ya ce tashar da Kamfanin Ezra ya fara ginawa tun cikin shekarar 2017, za ta taimakawa kasar mafi kankanta a duniya, wajen farfadowa, bayan shafe sama da shekaru 5 ana yaki.

Ya ce wannan aiki gagarumar nasara ce ga ma'aikatar makamashi da madatsun ruwa da ma kasar baki dayanta. Kuma abu mafi muhimmanci shi ne, ya ba su kwarin gwiwar cewa burinsu zai tabbata. Kana aikin zai bunkasa ci gaban bangarorin tattalin arziki.

Kashin farko na aikin tashar, zai samar da wutar lantarki mai karfin MW 33, kafin a kamala aikin baki daya a shekarar 2021.

Sudan ta Kudu na daga cikin kasashe mafi karancin wutar lantarki a duniya, inda kaso 90 na al'ummarta miliyan 12, ba sa samun lantarkin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China