Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar kawancen kasashen Larabawa ta bukaci Amurka ta cire sunan Sudan daga jerin kasashe masu daukar nauyin ta'addanci
2019-11-25 10:14:34        cri
Shugaban majalisar dokokin kungiyar kawancen kasashen Larabawa, Mishaal Bin Fahm Al-Salami, ya bukaci Amurka ta cire Sudan daga cikin jerin sunayen kasashen dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci.

Mishaal bin Fahm Al-Salami, ya bayyana bukatar ne cikin wasikar da majalisar ta aikewa mataimakin shugaban Amurka da shugaban majalisar dattawan kasar, Mike Pence da shugabar majalisar wakilai, Nancy Pelosi da sakataren harkokin wajen kasar, Mike Pompeo.

Sanarwar da majalisar ta fitar, ta ruwaito shugaban cikin wasikar, na shaidawa jami'an na Amurka kudurin da daukacin 'yan majalisar suka amince da shi a ranar 31 ga watan Oktoba, wanda ke neman a cire Sudan daga cikin jerin masu daukar nauyin ta'addanci.

Sanarwar ta kara da cewa, majalisar ta amince da kudurin ne la'akari da kokarin Sudan na yaki da ta'addanaci da fafutukar wanzar da zaman lafiya, tare da aiwatar da dukkan kudurorin da ta dauka cikin tsarin yaki da ta'addanci da kare hakkin bil adama da Amurka ta amince da su.

Tun a shekarar 1993, Amurka ta sanya Sudan cikin jerin kasashe masu daukar nauyin ayyukan ta'addanci, a lokacin kasar na karkashin mulkin Omar al-Bashir, wanda sojoji suka hambarar a watan Afrilun bana, biyo bayan zanga zangar da ta barke a kasar tun cikin watan Disamban bara.

Haramta cinikayyar da ta shafi makamai da bada taimakon kudi da nau'ika daban daban na haramci kan hada-hadar kudi, ciki har da karbar rance daga bankin duniya da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa, na daga cikin takunkuman da Amurka ta kakabawa kasashen dake cikin jerin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China