Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Sudan ta Kudu ya gana da Liu Xincheng
2019-12-12 13:39:47        cri
A ranar 10 ga wata, shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit ya gana da mataimakin shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin Liu Xincheng a birnin Juba, fadar mulkin kasar Sudan ta Kudu.

A yayin ganawar tasu, Liu Xincheng ya mika sakon gaisuwa na shugaba Xi Jinping ga shugaba Salva Kiir Mayardit. Ya ce, shugabannin biyu sun gana a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka yi a birnin Beijing, inda suka cimma matsayi daya kan wasu muhimman batutuwa. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan kasar Sudan ta Kudu wajen shimfida zaman lafiya a kasar, tana kuma fatan yin hadin gwiwa da kasar Sudan ta Kudu, wajen aiwatar da sakamakon taron FOCAC, domin daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi.

A nasa bangare kuma, shugaba Salva Kiir Mayardit ya yi fatan alheri ga shugaba Xi Jinping, ya kuma yaba dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tare da nuna godiya ga kasar Sin, dangane da taimakon da kasar Sin ta baiwa kasar Sudan ta Kudu, kan gina ababen more rayuwa, da kuma taimakon jin kai da kasar Sin ta samar wa kasarsa. Ya kara da cewa, kasarsa tana son yin hadin gwiwa da kasar Sin, domin inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Daga bisani kuma, Liu Xincheng ya gana da mukaddashin shugaban majalisar dokokin kasar Sudan ta Kudu da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China