Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta amince da dokar rusa tsohuwar jami'yya mai mulkin kasar
2019-11-29 11:04:21        cri

A yayin wani taron hadin gwiwa na majalisar gudanar da mulkin Sudan da majalisar ministocin kasar wanda ya gudanar a ranar Alhamis, an zartar da hukuncin rusa tsohuwar jami'yya mai mulkin kasar (NCP).

Firaministan kasar Abdalla Hamdok ya wallafa sako a shafinsa na Facebook dake cewa, "mun amince da wannan doka yayin wani taron hadin gwiwa da muka yi tare da takwarorinmu na majalisar mulkin kasar domin cikakkiyar aiki da dokar".

Hamdok ya kuma furta cewa, dokar ta amince a gudanar da adalci, da tabbatar da kare mutuncin jama'a, da karewa al'umma dukiyoyinsu, bugu da kari, dokar ta shafi samar da damar kwato dukiyar al'ummar kasar Sudan da aka sace.

Dokar da aka amince da ita ta shafi rusa tsohuwar gwamnati, da rusa jami'yyar NCP da dukkan rassanta.

Kundin tsarin mulkin kasar, wanda majalisar mulkin kasar da majalisar ministocin kasar suka amince da shi, ya nuna cewa, majalisar mulki da majalisar ministocin kasar suna da 'yancin zartar da doka har zuwa lokacin da za'a kafa majalisar dokokin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China