Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta yi ban kwana da cutar polio kafin shekarar 2020
2019-12-11 09:39:15        cri
Najeriya kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika tana fatan cimma nasarar kawo karshen cutar polio a shekarar 2020.

Faisal Shuaib, shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko ta Najeriya, ya shedawa manema labarai a Abuja cewa, sakamakon yadda kasar ke shirin ban kwana da cutar, irin jajurcewar da ma'aikata masu yaki da cutar polio a dukkan matakai na kasar suka nuna tilas ne a yaba musu.

A halin yanzu, tawagar jami'an hukumar tantancewa shiyyar Afrika na hukumar lafiyar ta duniya (WHO) suna Najeriya domin duba yadda kasar ke shirye shiryen kawo karshen cutar ta polio kafin watan Yunin shekarar 2020.

Jami'in ya ce, wakilan zasu kai ziyarar tantancewa zuwa sassan kasar biyu. Da farko zasu ziyarci jahohin kudancin kasar daga ranar 9-20 ga watan Disamba, sai kuma jahohin arewacin kasar daga ranar 2-13 ga watan Maris na shekarar 2020.

A cewar jami'in, sun himmatu matuka, kuma ya bada tabbatacin bada fifiko game da aikin kawo karshen cutar polion daga Najeriya. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China