Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya gabatar da sunan sabon shugaban hukumar tattara haraji ga majalisar dattijai
2019-12-10 11:09:06        cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya gabatar da sunan Muhammad Nami, a matsayin wanda zai nada sabon shugaban hukumar tattara haraji na kasar ko FIRS, ga majalissar dattijan kasar domin tabbatarwa. Shugaba Buhari ya gabatar da Nami ne a matsayin wanda zai maye gurbin Tunde Fowler, wanda wa'adin aikin sa ya kare a jiya Litinin.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta bayyana sabon shugaban hukumar ta FIRS a matsayin gogaggen ma'aikaci, masanin tattara haraji, akawu kuma mai ilimin jagoranci, wanda ya jima yana aiki a wannan fanni. Nami, ya shafe kusan shekaru 30 yana aiki a fannin tantance hada hadar kudade, da karbar haraji da dai sauran su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China