Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan fashin teku sun yi garkuwa da matuka jirgin ruwa 19 a gabar tekun Najeriya
2019-12-06 11:15:11        cri
Hukumar kula da harkokin tekun Najeriya NIMASA, ta bayar da tabbacin yin garkuwa da ma'aikatan jirgin ruwa 19 a lokacin da 'yan fashin teku suka afkawa jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kasar.

NIMASA ta bayyana cikin wata sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labaru na Xinhua kwafenta a birnin Abuja cewa, jirgin ruwan mai suna "Nave Constellation," yana makare da mai a lokacin da barayin suka afka masa.

Hukumar ta NIMASA ta ce, wasu mutane 9 daga cikin matuka jirgin ruwan ba'a taba lafiyarsu ba kuma babu wata illa da 'yan fashin tekun suka yiwa jirgin ruwa a lokacin da suka kai masa farmaki a ranar Talata a waje mai tazarar mil 77 daga tsibirin Bonny Island dake yankin Niger Delta shiyyar kudancin Najeriya.

Sai dai ba'a tantance asalin kasashen da 'yan fashin tekun suka fito ba.

Bonny Island daya ne daga cikin wuraren da ake lodin danyen mai a Najeriya, kasa mafi arzikin mai a nahiyar Afrika.

NIMASA ta ce matuka jirgin ruwan sun tuntubi hukumomin kula da tekun Najeriya da sojojin ruwan kasar, inda suka gaggauta kai dauki domin ceto matuka jirgin ruwan wadanda 'yan fashin tekun ba su yi nasarar yin awon gaba da su ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China