Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan majalissar dimokarat sun fitar da daftari biyu game da shirin tsige shugaba Trump
2019-12-11 10:15:41        cri

'Yan majalissar wakilan Amurka daga jam'iyyar dimokarat, sun fitar da daftari biyu game da shirin tsige shugaba Trump daga mukaminsa, suna masu kafa hujja da yadda shugaban ya yi amfani da ofishin sa ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma yin karan-tsaye ga aikin majalisar.

Da yake tsokaci game da hakan, shugaban kwamitin shari'a na majalissar Jerry Nadler, wanda kakakin majalissar Nancy Pelosi ta rufawa baya, tare da sauran shugabannin kwamitocin majalissar daga jam'iyyar dimokarat, ya ce shugaba Trump ya ci gaba da karya doka, wanda hakan ya tilasawa majalissar daura damarar tsige shi.

Shi ma a nasa tsokaci, shugaban kwamitin tattara bayanan sirri Adam Schiff, cewa ya yi akwai tarin hujjoji na karya dokar kasa masu nasaba da mu'amalar shugaba Trump da kasar Ukraine, dake tabbatar da wajibcin tsige shi. Ya ce bayan da aka tabbatar da hakan, sai kuma ya sake aikata wani laifi, wato ya yi kokarin dakile binciken da ake yi.

To sai dai kuma a martanin da ya gabatar ta sakon twitter, shugaba Trump ya ce tsige shugaban kasa wanda ya samar da sakamako mai kyau, ciki hadda bunkasa tattalin arziki wanda ba shi da na biyu a tarihi, shugaban da ya zamo zakaran gwajin dafi mafi nasara da Amurka ta taba samarwa, kuma wanda bai aikata wani laifi ba, rashin hankali ne a siyasance. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China