![]() |
|
2019-12-04 11:29:07 cri |
Kuri'u 13 na mambobin sun amince, yayin da mambobi 9 ba su goyi baya ba, da kwamitin tattara bayanai wanda ke karkashin jagorancin Adam Schiff ya mika rahoton binciken ga kwamitin harkokin shara'a na majalisar dokokin wanda zai jagoranci duba binciken neman tsige shugaban kasar kuma shi ne ke da alhakin tsara dukkan jadawalin matakan tsige shugaba Trump daga mukaminsa.
Kada kuri'ar na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar demokarat suka fitar da wani rahoto dake neman hujjoji game da zargin da ake yiwa mista Trump na aikata ba daidai ba da neman kawo cikas ga taron majalisar. Ta hanyar amfani da dan majalisa na jam'iyyar Republican Mark Meadows, wanda na hannun daman shugaba Trump ne, ya mayar da martani cikin gaggawa a sakon da ya wallafa ta shafinsa na twita game da kada kuri'ar, inda ya bayyana yunkurin tsige shugaban da cewa babu hujja, kuma siyasa ce karara. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China