Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Nuna bambancin jinsi ya kawo cikas ga aikin kiyaye hakkin mata a Amurka
2019-11-26 13:54:06        cri

Kungiyar nazarin hakkin Bil Adama ta kasar Sin, ta ba da wani bayani mai taken "Yadda aka dade ake fuskantar matsalar nuna bambancin jinsi a Amurka na dakile aikin kiyaye hakkin mata a kasar". Bayanin ya fayyace cewa, har illa yau Amurka ba ta sa hannu kan yarjejeniyar kawar da bambancin da aka nuna ga mata ba, wanda MDD ta gabatar don tabbatar da hakkin Bil Adama. Matakin dai ya nuna cewa, matsalar nuna bambancin jinsi a kasar Amurka na kawo babbar illa ga kiyaye hakkin mata a kasar.

Bayanin ya kuma nuna cewa, an dade ana nuna bambanci ga mata a Amurka a fannoni daban-daban, musamman ma a fannin tattalin arziki, kuma matsalar nuna wa mata karfin tuwo ta kara tsananta, kuma babu tabbaci game da hakkin kiwon lafiyar jikin matan kananan kabilu a kasar.

Dadin dadawa, bayanin ya ce, Amurka na da fuska biyu kan batun hakkin Bil Adama, inda a sa'i daya take fakewa da batun a matsayin matakin tsoma baki da zargi kan sauran kasashe. A sa'i daya kuma, ta yi biris da halin da take ciki a wannan fanni a cikin gida, ciki hadda matsalar nuna bambancin jinsi. Abubuwan da Amurka ke yi sun kawo babbar illa ga aikin tabbatar da hakkin Bil Adama a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China