![]() |
|
2019-12-05 11:06:10 cri |
Uwargida Tallen ta yi wannan kiran ne, mako guda bayan da hukumar yaki da fataucin bil-Adam ta kaddamar da wani gangamin ilimantar da jama'a, game da yaki da masu cin zarafin mata ta hanyar lalata, ta hanyar kaddamar da wani kundin da za a rika wallafa sunayen mutanen da ke aikata wannan danyen aiki.
Ta bayyana cewa, a kalla kananan yara mata 'yan Najeriya miliyan 2 ne suke fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata a shekara, kuma kaso 28 cikin 100 ne kawai na wannan adadi suka kai rahoto.
A don haka ta ce, ya dace a rika zartar da hukunci mai tsanani kan masu aikata wannan laifi. Ta kuma yi kira ga kafofin watsa labarai, da su rika ba da rahoton batutuwan da suka shafi mata, yara da mutane masu rauni.
Wani rahoto da asusun tallafawa yara na MDD (UNICEF) ya fitar, na nuna cewa, 1 cikin 4 na yara mata da kuma yaro daya cikin 10 a Najeriya, sun taba fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China