Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu nasarar saka karafa na farko kan babban ginin da ake yi a sabuwar hedkwatar Masar
2019-11-18 13:49:19        cri

A karshen makon jiya, reshen kamfanin gini na CSCEC na kasar Sin da ke kasar Masar ya samu nasarar saka karafa na farko kan babban ginin da yake ginawa, kuma zai kasance a matsayin alamar yankin kasuwanci dake tsakiyar sabuwar hedkwatar kasar Masar. Hakan ya alamta cewa, an shiga sabon mataki na aikin babban ginin da zai zama gini mafi tsayi a Afirka. Kusoshin gwamnatin Masar da na kamfanin CSCEC sun halarci bikin.

Ministan kula da wuraren kwana na kasar Masar ya bayyana cewa, wannan babban gini zai kasance gini mafi tsayi a nahiyar Afirka, kana baya ga zama alamar yankin kasuwanci dake tsakiyar birnin, zai kuma kasance wata alamar kasar ta Masar. Ginin zai zama alamar tunawa da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Masar da Sin. Babban jami'in ya kara da cewa, shugaba Abdel Fattah al Sisi na Masar ya yaba wa ci gaban kafa yankin kasuwanci dake tsakiyar birnin, ya kuma bukaci sassa daban daban masu ruwa da tsaki da su inganta hada kai da kasar Sin, a kokarin kafa yankin cikin hadin gwiwa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China