Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta kama hanyar cin nasarar yaki da cutar shan inna
2019-12-04 09:24:51        cri
Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta Nijeriya, ta ce kasar ta kama hanyar cin nasara kan yaki da cutar shan inna cikin kankanin lokaci.

Yayin wani taro a Abuja, babban birnin kasar, domin nazarin aikin riga kafin cutar shan inna a kasar, hukumar ta ce shekaru uku ke nan ba tare da an samu barkewar cutar a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika ba, lamarin dake zaman gagarumar nasara.

Shugaban hukumar, Faisal Shua'aib, ya ce kasar ta kama hanyar fattakar cutar baki daya. Sai dai, akwai bukatar jami'an lafiya su samu damar shiga wasu yanukunan jihar Borno da wasu sassan yankin arewa maso gabashin kasar dake fama da rashin tsaro.

Ana sa ran kwararru mahalarta taron na yini biyu, su yi bitar kokarin da Nijeriya take yi wajen fattakar cutar da kuma gano gibin dake akwai.

A cewar shugaban, an samu nasara wajen kai wa ga yara dake yankuna da ba a iya shiga, da ci gaba da wayar da kan al'umma da karfafa ayyukan ba da riga kafi a kai a kai.

Jami'in ya kara da cewa, za a iya cimma nasara a aikin fattakar cutar shan inna daga kasar, yana mai bayyana imanin cewa, nan bada dadewa ba, Nijeriya za ta karbi shaidar fattakar cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China