Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta kaddamar da sabon shirin tabbatar da tsaro domin magance kalubale masu tasowa
2019-12-05 09:57:43        cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da wani shirin kan tabbatar da tsaro da aka yi wa gyaran fuska, domin magance kalubale masu tasowa a kasar mafi yawan al'umma a Afrika.

Shirin na tabbatar da tsaron kasa, daftari ne da ake bitarsa bayan shekaru 5, wanda ya kunshi cikakkun bayanai kan yadda kasar za ta inganta karfin rundunar sojinta da sauran hukumomin tsaro.

Da yake jawabi yayin kaddamar da daftarin shirin a Abuja, babban birnin kasar, Muhammadu Buhari ya ce gwamnati za ta ci gaba da inganta tsaron al'ummar Nijeriya ta hanyar inganta tsaro a zahiri.

Ya ce kalubalen tsaro da dama da kasar ke fuskanta ne ya sa aka samar da cikakkun kuma ingantattun hanyoyin tunkararsu ta kowacce fuska.

Ya ce yayin da ake ci gaba da kokarin kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin arewa maso gabashin kasar, da kuma aza tubulin samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a yankin, suna kuma kokarin shawo kan rikicin makiyaya da manoma, da fashi da makami da nau'ika daban daban na kalubalen tsaro. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China