Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Karin mutanen Syria na matukar amfana da shirin jin kan bil adama wanda ya ratsa kan iyakokin kasashe
2019-12-10 10:36:39        cri
Kakakin MDD ya ce a halin yanzu al'ummar Syria suna matukar cin gajiyar shirin tallafin jin kan bil adama sama da wanda suka taba samu a lokutan baya.

A watan Nuwamba kadai, MDD ta samarwa mutane sama da miliyan 1.1 kayan abinci ta hanyar shirin bada jin kai da ya ratsa kan iyakokin kasashe, kuma an ninka adadin a watan Janairu, in ji Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres.

Kayayyakin tallafin sun hada da magunguna da aka aike da su daga Iraki zuwa arewa maso gabashin Syria, an samar da tallafin wanda ba'a taba samarwa mutanen yankin makamancinsa ba, Dujarric ya bayyana hakan ne a taron manema labarai.

Kimanin mutane miliyan 4 dake bukatar tallafi a yankin arewacin Syria ne suka samu tallafin jin kai na MDDr karkashin shirin tallafin wanda ya ratsa kan iyakokin kasashe, wanda ya hada da mutane miliyan 2.7 a arewa maso gabashi wadanda rayuwar kacokan ta dogara kan ayyukan bada jin kan al'umma, in ji Dujarric.

Shirin bada tallafin wanda ya ratsa kan iyakokin kasashe a Syria shi ne shiri mafi inganci a duniya. MDDr za ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da ingancin ayyukan bada jin kan bil adama, a cewar kakakin MDDr. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China