Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya karfafawa IAEA gwiwa wajen inganta amfani da makamashin nukiliya
2019-11-12 11:10:40        cri
Jakadan kasar Sin a MDD ya karfafawa hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato (IAEA) gwiwa, da ta kara azama wajen kyautata makamashin nukiliya don amfani na zaman lafiya.

Bayan kammala sauraren rahoton aikin hukumar, mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Wu Haitao ya ce, inganta ci gaban makamashin nukiliya na kasa da kasa da kuma fadada amfani da fasahar nukiliyar suna taka muhimmiyar rawa wajen kyautata yanayin rayuwa da bunkasuwar tattalin arziki, kana da tabbatar da tsaron ingancin makamashi da kuma magance matsalolin sauyin yanayi.

A game da hakan, ya jaddada bukatar IAEA ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ganin ana amfani da makamashin nukiliyar ta hanyar zaman lafiya.

Wu ya ce, ya kamata hukumar ta yi la'akari da yanayin bukatun da mambobin kasashen ke da shi wajen raya ci gaban makamashin nukiliyar, da samar da kudade, kana ta ci gaba da bayar da goyon baya ga mambobi kasashen wajen bunkasa amfani da makamashin nukiliyar, sannan a fadada amfani da fasahar nuliya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China