Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana damuwa game da taazzarar rikici a Libya
2019-12-03 10:41:50        cri

Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana damuwa game da ta'azzarar rikici a Libya a baya-bayan nan, yana mai kira ga dukkan bangarorin kasar su yayyafawa yanayin ruwan sanyi tare da tsagaita bude wuta.

Mambobin kwamitin sun bayyana damuwarsu ne musamman kan rahotannin keta takunkuman makamai da karuwar shigar dakarun haya cikin rikicin kasar.

Sun yi kira ga dukkan kasashe mambobin MDD, su yi cikakkiyar biyayya ga takunkumin makaman kamar yadda kudurin majalisar na 1970 ya tanada. Sun kuma yi kira ga kasashen da kada su tsoma baki cikin rikicin ko daukar wani mataki da zai iya kara rura wutar rikicin.

Kwamitin ya kuma bayyana goyon bayansa ga shugabanci da aikin Ghassan Salame, manzon musamman na Sakatare Janar na MDD kan batun Libya, kuma shugaban shirin wanzar da zaman lafiya na majalisar a kasar.

Ya kuma jaddada goyon bayansa ga kokarin da kasashen duniya ke yi na mara baya ga Ghassan Salame, don ingiza aiwatar da tsarin siyasa karkashin jagorancin kasar, wadda MDD ta samar da hadin gwiwar kasashe mambobinta da kuma bangarorin Libyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China