Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira da a dauki mataki kan narkewar tsaunika masu kankara da samar da ruwa mai dorewa
2019-11-01 14:24:32        cri
Taro kan tsaunika na farko da hukumar kula da yanayi ta duniya da abokan huldarta suka gudanar, ta yi kira da a dauki mataki yayin da ake fuskantar narkewar tsaunika masu kankara.

Taron na yini 3, wanda aka kammala a jiya, ya bayyana matakan da ya kamata a dauka wajen taimakawa kara samun ci gaba mai dorewa da rage aukuwar annoba da tunkarar sauyin yanayi a yankunan tsaunika da kuma kasa.

Har ila yau, taron ya bayyana damuwa game da yadda wadatar ruwa ke zama gagarumin kalubale ga al'ummar duniya.

Yankunan tsaunika ne suka mamaye 1 bisa 4n yankin ban kasa, wanda kuma mazauni ne ga mutane kimanin biliyan 1.1, kuma ana kiransu da ma'adanar ruwa ta duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China