Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kasar Sin ya yi kira da a samar da hanyoyi a kasashe masu tasowa da ba sa kusa da gabar ruwa
2019-12-06 10:34:14        cri
Mataimakin wakilin din-din-din na kasar a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa, da su yi kokarin hade kasashe 32 masu tasowa (LLDC) da ba sa kusa da gabar ruwa da hanyoyi masu kyau.

Wu Haitao ya yi wannan kiran ne, yayin zaman bitar tsakiyar wa'adi kan aiwatar da shirin da aka cimma a Vienna (VPOA) game da wadannan kasashe na shekarar 2014-2024. Ya ce, shirin na VPOA, ya ga irin nasarroin da aka samu shekaru biyar bayan aiwatar da shirin, amma kuma ba dukkan kasashen ne suka amfana da shirin ba. Don haka, ya kamata kasa da kasa su ci gaba da kokarin ganin an aiwatar da shirin kamar yadda aka tsara.

Wu ya bayyana yayin zaman bitar yadda aka aiwatar da shirin da babban zauren MDD ya gudanar a jiya cewa, akwai bukatar duniya ta dauki matakai na ganin an gina alakar kasa da kasa da za ta hade wadannan kasashe da hanyoyi masu dacewa.

A shekarar 2014 ne, babban taron MDD na biyu game da kasashen na LLDC ya amince da shirin na Vienna (VPOA) da nufin samar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa da rage talauci da tabbatar da ganin an hade wadannan kasashe cikin tsarin tattalin arziki na duniya. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China