Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya yi Allah wadai da harin masallaci a Burkina Faso
2019-12-03 09:56:50        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da babbar murya game da harin da aka kaddamar ranar Lahadi a wani coci a kasar Burkina Faso

A sanarwa da kakakin babban sakataren Stephane Dujarric ya ce, Guterres ya yi amanna cewa kamata ya yi wuraren bauta su kasance wurare mafiya daraja da zaman lafiya, bai dace su zama wuraren zubda jini da ayyukan ta'addanci ba, kuma tilas ne a baiwa mutane dama su gudanar da addininsu cikin kwanciyar hankali.

Mista Guterres ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da jama'ar kasar da kuma gwamnatin kasar Burkina Faso. Sannan ya yi fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka.

Kimanin mutane 14 aka tabbatar da mutuwarsu kana wasu da dama sun samu raunuka bayan da wasu 'yan bindiga suka bude wuta ga taron masu ibada a cocin yankin Hantoukoura dake gabashin Burkina Faso

Tun da farko a ranar Litinin, Miguel Moratinos, babban jami'in hukumar MDD, shi ma ya yi Allah wadai da harin ta'addanci a kasar ta shiyyar Afrika.

A cewar kakakinsa Nihal Saad, Moratinos ya jaddada cewa, duk wani nau'in cin zarafi ko hare-haren ta'addanci da ake kaiwa kan masu ibada ko kuma wuraren ibadar al'amari ne da ba za'a taba amincewa da shi ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China