Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da bikin aladun gargajiya na Sin da Afrika karo na 4 a Masar
2019-10-28 10:08:01        cri

An kaddamar da bikin al'adun gargajiya na Sin da Afrika karo na 4 jiya Lahadi a wani wurin ibada mai dadadden tarihi mai suna Philae Temple dake jihar Aswan ta kasar Masar.

Ana gudanar da bikin da ya kunshi nuna wasannin kungiyoyin raye-raye daga kasashe 30, wanda kuma zai kai har ranar 31 ga wata ne karkashin ma'aikatar kula da al'adu ta Masar, da hadin gwiwar sauran ma'aikatu da suka hada da na yawon bude ido da kayayyakin gargajiya da mai kula da matasa da wasanni da mai kula da shige da fice da kuma na hadin kan al'umma.

Ministan kula da al'adu na Masar, Inas Abdel-Dayem, ya bayyana yayin bude taron cewa, bikin wani bangare ne na ci gaba da raya dangantaka mai zurfi dake tsakanin Sin da Masar da ma Sin da nahiyar Afrika baki daya.

Bikin ya samu halartar ministocin Masar da jami'ai da 'yan majalisa da masu fasahohi da taurarin fina-finai.

Kungiyar masu rawar gargajiya ta Little Egert ta birnin Xiamen na kasar Sin ne suka fara bude bikin da wasanninsu, daga baya kuma kasashen Uganda da Sudan da Namibia da Algeria da Tunisia da Afrika ta kudu da sauransu, suka gabatar da nasu salon rawar.

Soheier Abel-Qader, wadda ta kirkiro kuma take shugabantar bikin, ta ce alaka ta kut da kut dake tsakanin kasar Sin da Masar da kuma nahiyar Afrika ne ya ba ta kwarin gwiwar shirya bikin da nufin inganta al'adun bangarorin biyu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China