Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta tsawaita wa'adin aikin sojojin kiyaye zaman lafiya dake Darfur
2019-11-01 14:24:12        cri
Jiya Alhamis, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin tsawaita wa'adin aiki na rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya wadda MDD da kungiyar tarayyar kasashen Afirka suka tura zuwa birnin Darfur na kasar Sudan zuwa ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar 2020.

Kudurin din ya bukaci gwamnatin kasar Sudan, kungiyoyin dake dauke da makamai a yankin Darfur da sauran bangarorin da abin ya shafa da su dukufa wajen shimfida zaman lafiya a yankin, domin samar da yanayi mai kyau ga rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na janyewa daga wannan yanki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China