Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar musulmi ta Sin da ta jihar Xinjiang sun bayar da sanarwa game da dokar hakkin Bil Adama kan yankin da Amurka ta zartas
2019-12-05 11:28:17        cri

Kungiyar musulmi ta kasar Sin ta bayar da sanarwa game da dokar hakkin Bil Adama kan yankin Xinjiang na Uygur da Amurka ta zartas, inda ta nuna matukar rashin jin dadi da kin amincewa.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, gwamnatin kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar tabbatar da bin addini cikin 'yanci. Bisa kundin tsarin mulkin kasar da dokokin yankunan kabilun kasar, ana girmama da tabbatar da kare 'yancin bin addini na al'ummomin kabilu daban-daban na jihar Xinjiang. Tun daga shekarun 1990, kungiyoyin uku wato 'yan aware, da masu tsattsauran ra'ayi, da 'yan ta'adda na kasar Sin da na kasashen waje sun hada kai da yin amfani da addini don zuga jama'a da yada tunanin tsattsauran ra'ayi da tuzura jama'a su shiga ayyukan ta'addanci.

An kafa cibiyoyin koyar da sana'o'i a jihar Xinjiang bisa dokoki, inda ake gudanar da ayyuka don kawar da ta'addanci da tsattauran ra'ayi, da hana faruwar ayyukan ta'addanci, a kokarin tabbatar da kare 'yancin rayuwa na jama'ar kabilu daban daban, da kiwon lafiya, da samun bunkasuwa da sauransu, kuma wannan mataki ya samu nasara. Sin ta kalubalanci kasar Amurka da ta girmama hakihakin halin da ake ciki a yankin, da dakatar da aikin tsoma baki a harkokin cikin gida na kasar Sin da kawo illa ga jama'ar kasar Sin.

Hakazalika kuma, kungiyar musulmi ta jihar Xinjiang tana adawa da ma Allah wadai da dokar hakkin Bil Adama kan yankin Xinjiang na Uygur da Amurka ta fitar, ta yi nuni da cewa, wannan doka ta yi watsi da yanayin zaman lafiya da ci gaban kiyaye hakkin bil Adama da aka samu a yankin na Xinjiang, inda ta zargi matakan da gwamnatin jihar Xinjiang ta dauka wajen yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, ta kuma rika bayar da labarai marasa tushe.

A tsawon shekaru uku da suka gabata, an samu zaman lafiya da wadata da hadin kan kabilu da kuma bin addini cikin lumana bisa doka a jihar Xinjiang, hakan tamkar mayar da martini ne ga zargi maras tushe da Amurka ta yi game da ci gaban da aka samu a Xinjiang. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China