Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin kare hakkin bil Adama na Sin sun bayar da sanarwoyi game da dokar hakkin Bil Adama kan yankin Xinjiang da Amurka ta zartas
2019-12-05 11:30:04        cri

Asusun kare hakkin bil Adama na kasar Sin da kungiyar nazarin hakkin dan-Adam ta kasar Sin sun bayar da sanarwoyi daya bayan daya game da dokar hakkin Bil Adama kan yankin Xinjiang na Uygur da Amurka ta zartas, inda suka yi nuni da cewa, wasu 'yan siyasa na kasar Amurka sun kau da kai kan yadda aka raunata da ma kashe jama'a sakamakon ayyukan ta'addanci a jihar Xinjiang, gami da nasarorin da aka samu wajen yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi da kare hakkin bil Adama a jihar.

Amincewa da wannan doka da 'yan siyasar Amurka suka yi, ya shaida cewa, ba su damu da batun kare hakkin bil Adama ba, suna da wata manufa ce ta daban, wato fakewa da batun yankin Xinjiang, wajen kawo illa ga mutuncin kasar Sin, da zaman lafiyar kasar, da kuma hana bunkasuwar kasar. Sanarwar ta yi kira ga kasashen duniya, da su fahimci hakikanin manufar kasar Amurka kan batun hakkin bil Adama, da kara fahimtar hakikanin yanayin da kasar Sin ke ciki.

Kungiyar binciken hakkin bil Adama ta kasar Sin ta nuna kin amincewa da yin Allah wadai da wannan doka da Amurka ta zartas, ta yi nuni da cewa, ba a samu lamarin ta'addanci har na tsawon shekaru 3 a jihar Xinjiang ba, ana samun zaman lafiya da hadin kan kabilu da bin addini cikin lumana da kuma jin dadin rayuwar jama'a a yankin, kana an tabbatar da kare hakkin jama'a a fannoni daban daban. Game da yanayin hakkin bil Adama da ake ciki a yankin Xinjiang, al'ummomi kabilu daban daban dake rayuwa a yankin su ne ke da ikon bayyana ra'ayoyinsu kan batun. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China