![]() |
|
2019-12-06 09:32:42 cri |
Kakakin ma'aikatar tsaron Sudan Amer Mohamed Al-Hassan, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, jami'an sojoji masu binciken sirri sun mika mayakan Boko Haram 6 wadanda suke dauke da takardun fasfo na kasar Chadi a cikin yankunan kasar Sudan.
Ya kara da cewa, daga bisani an mika mutanen da aka cafke ga hukumomin tsaron N'djamena karkashin tsarin yarjejeniyar hadin gwiwar tsaron kan iyakoki wanda kasashen Sudan, Libya, Nijer da Chadi suka rattabawa hannu.
Tun daga shekarar 2008, kungiyar Boko Haram ta fara kaddamar da ayyukanta a kasashen dake makwabtaka da Najeriya.
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China