Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin Najeriya ta hallaka mayakan Boko Haran 3 a Gwoza
2019-09-13 16:04:05        cri
Kakakin rundunar sojojin Najeriya Sagir Musa, ya ce dakarun rundunar sun hallaka wasu mayakan Boko Haram 3, a karamar hukumar Gwoza dake jihar Borno, ta arewa maso gabashin kasar.

Jami'in na soji ya ce a ranar Laraba, sojoji da dakarun sa kai masu tallafawa ayyukan tsaro ko Civilian JTF, sun yi hadin gwiwar gudanar da harin kakkabe gyauron mayakan kungiyar daga yankin.

Ya ce an yi musayar wuta da 'yan Boko Haram a yankin Kirawa dake karamar hukumar ta Gwoza, wanda ya sabbaba kisan mayakan kungiyar, yayin da wasu kuma suka tsere. To sai dai kuma ya ce ba bu wani jami'in soji da ya rasu, ko ya jikkata yayin artabun. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China