Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ICRC: Hare haren Boko Haram sun sabbaba batan 'yan Najeriya 22,000
2019-09-13 15:49:42        cri
Hukumar bayar da agaji ta Red Cross, ta ce akwai kusan 'yan Najeriya da yawansu ya kai 22,000 da har yanzu ba a san inda suke ba, a yayin da aka kwashe fiye da shekaru 10 ana fuskantar hare haren kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban hukumar ta Red Cross ko ICRC Peter Maurer, ya ce wannan ne alkaluma mafi yawa da aka taba samu a wata kasa.

Maurer, ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki 5 da yake gudanarwa a Najeriya. Yayin ziyarar babban jami'in na Red Cross ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da manyan jami'an gwamnati, da wakilan kungiyoyin fararen hula, da wasu manyan 'yan kasuwa.

Kaza lika Mr. Maurer ya zanta da iyalai, da 'yan uwan wasu da suka bace sakamakon irin wadannan tashe tashen hankula a Maiduguri da Monguno dake jihar Borno, jihar da ita ce babbar tungar kungiyar ta Boko Haram.

Ya ce ICRC na yin hadin gwiwa da Najeriya, wajen aiwatar da dabaru daban daban, domin gano wadanda suka bace, matakin da ya kai ga warware irin wadannan matsaloli kimanin 367, tun fara aiwatar da shirin a shekarar 2013. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China