Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta tabbatar da tsaron abinci
2019-05-13 19:50:37        cri

Mataimakin shugaban cibiyar kimiyar aikin gona ta kasar Sin Mei Xurong ya bayyana cewa, kasar Sin za ta cimma ka'idojin da ake bukata na samar da isasshen hatsi da ma tsaron abinci baki daya.

Mei ya kuma bayyana cewa, isasshen abinci shi ne zai tabbatar da gina al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni nan da shekarar 2020 da ma burin da kasar Sin ke fatan cimmawa nan da shekarar 2035 na kasa mai bin salon gurguzu na zamani.

Jami'in ya bayyana hakan ne, yayin taron dandalin tsara manufofin aikin gona na kasar da ma duniya baki daya da ya gudana a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Wani rahoton sashen raya aikin gona na kasar Sin na shekarar 2019 da Mei ya fitar, ya bayyana cewa, tsarin aikin gona da ke samar da abinci, ya ba da gudummawar kimanin kaso 23.3 cikin 100 na GDPn kasar, da kuma kaso 36.07 cikin 100 na guraben ayyukan yi a kasar, abin da ke zama kashin bayan tattalin arzikin kasar ta Sin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China