Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai na samar da isassun guraben aiki
2019-08-12 10:58:33        cri
Kididdigar da ma'aikatar kula da kwadago da ba da tabbaci ga al'umma ta fitar ta nuna cewa, a watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, yawan al'ummar birane da garuruwa da suka samu guraben aikin yi ya kai miliyan 7 da dubu 370, adadin da ya kai kaso 67% na burin da ake fatan cimmawa a wannan shekara gaba daya. Taron majalisar gudanarwar kasar ya kuma yi nuni da cewa, ya kamata a kara daukar matakai masu inganci na samar da guraben aikin yi, musamman ma a gabatar da manufofi na tallafawa daliban da suka kammala karatu a jami'o'i da sojojin da suka yi ritaya wajen samun ayyukan yi.

Yanzu haka lokaci ne da daliban jami'o'in da dama suka kammala karatunsu suke kuma neman aikin yi. Shugabar sashen kula da samar da guraben aikin yi ta ma'aikatar kwadago da ba da tabbaci ga al'umma, Madam Zhang Ying ta bayyana cewa, yawan daliban da suka kammala karatu a jami'o'in kasar Sin a wannan shekara ya kai miliyan 8 da dubu 340, kuma yanzu haka ana samar musu da guraben aiki yadda ya kamata. Nan gaba kadan, ma'aikatar za ta gudanar da ayyuka a fannoni da dama, don taimaka musu wajen samun guraben ayyuka.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China