2019-05-09 09:09:37 cri |
Wani rahoto da ma'aikatar aikin gona da raya yankunan karkara ta kasar Sin ta fitar, ya bayyana cewa, cinikayyar amfanin gona ta Intanet a shekarar 2018 da ta gabata, ta karu zuwa kaso 33.8 cikin 100, inda ya kai yuan biliyan 230.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 34.06.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, a shekarar 2018, harkokin cinikayya ta intanet sun dauki kaso 7.3 cikin 100 na ribar aikin gonar kasar, karuwar kaso 0.8 cikin 100 kan na shekarar da ta gabace ta.
Da yake karin haske, shugaban sashen harkokin kasuwa da bayanan tattalin azriki na ma'aikatar Tang Ke, ya bayyana cewa, aikin gona na zamani ya kankama, yayin da a hannu guda kuma jama'a sun yi amfani da bayanai game da fashohin sadarwa na zamani a bangaren aikin gona. Musamman, yadda aka samu karuwar amfani da muhimman bayanai wajen yanke shawara, kula da gonaki da sayar da albarkatun gona.
Ya ce, a karshen shekarar 2018, an kafa cibiyoyin samar da bayanai ga manoma 272,000 a sassan kasar, inda suke samar da hidimar bayanai, bincike kan manufofi da samar da horo kan fasahar sadarwa ta zamani a yankunan karkara.
Wadannan cibiyoyin samar da bayanai na yankunan karkara, na daga cikin matakai na baya-bayan da kasar Sin ta dauka na inganta matakan samun bayanai da fasahar sadarwar zamani a yankunan karkarar kasar, ta yadda za a rage gibin dake tsakanin birane da yankunan karkara.
Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin tana shirin yayata gina irin wannan cibiyoyi, inda za a mayar da hankali kan yankunan dake fama da talauci, ta yadda za a karade hedkwatocin kauyukan kasar nan da karshen wannan shekara.(Ibrahin)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China