Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 2 sun mutu yayin da wasu da dama suka kone biyo bayan fashewar kurtun gas a Nijeriya
2019-11-29 10:10:57        cri
An tabbatar da mutuwar mutane 2, yayin da wasu 23 suka kone, biyo bayan fashewar kurtun gas a jihar Lagos, dake kudu maso yammacin Nijeriya, a jiya Alhamis.

Wani babban jami'in bada agajin gaggawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a unguwar Ajegunle mai cunkoson Jama'a, dake kusa da yankin Lagos Island, ya ce lamarin ya auku ne sanadiyyar fashewar kurtun gas, biyo bayan yoyewar iskar gas din.

Femi Oke-Osanyintolu, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos, ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su sun kone, inda a garzaya da su asibitin gwamnati dake babban yankin jihar.

Jami'in ya ce an killace baki dayan yankin, sannan kuma ana gudanar da bincike. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China