Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin Najeriya zata tabbatar da tsaro a lokacin hutun kirsimeti a fadin kasar
2019-11-28 10:39:42        cri
Jami'in rundunar sojojin Najeriya ya sanar da cewa, hukumar tsaron ta dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da nufin dakile ayyukan bata gari a lokutan bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara dake tafe.

Aminu Iliyasu, kakakin rundunar sojojin Najeriyar ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, hukumomin tsaron kasar sun gudanar da atisayen sojoji masu yawa da nufin dakile dukkan barazanar ayyukan bata gari don hana su samun sukuni.

Aminu ya ruwaito babban hafsan sojojin Najeriyar Tukur Buratai yana cewa, dakarun sojojin za su cigaba da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan lokutan shagulgulan na wannan shekara a kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China