2019-11-29 10:04:40 cri |
Da yake kaddamar da shirin ayyukan gwamnati ta intanet, da ake sa ran zai jagoranci aikin komawa amfani da fasahohin zamani, yayin bikin bude babban taron intanet na kasar na bana Muhammadu Buhari, ya ce sauya tsarin tattalin arziki zuwa na zamani ba zabi ba ne, yana mai cewa abu ne da ya zama tilas.
Ya ce gabatar da ayyukan gwamnati ta kafar intanet zai kara taimakawa nasarorin da aka samu kawo yanzu da kuma kara musayar ayyuka tsakanin ma'aikatu da sassa da hukumomin gwamnati daban-daban.
A cewarsa, muhimmin abun da ake bukata ga shirin na gwamnati shi ne, dukkan cibiyoyinta su samar da tawagar kula da aikin komawa amfani da fasahohin zamani da za ta yi aiki da ma'aikatar sadarwa domin tabbatar da aiwatar da ayyuka da dabaru da shirye-shiryen gwamnati ba tare da tangarda ba. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China