Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun Nijeriya sun kashe mayakan BH 13
2019-11-30 15:37:58        cri
A kalla mayakan BH 13 aka kashe, lokacin da sojoji suka dakile yunkurin kungiyar ta kai hari a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Kakakin rundunar sojin Nijeriya a yankin arewa maso gabashin kasar, Aminu Iliyasu, ya ce sojojin Nijeriya da na Kamaru ne suka dakile yunkurin harin na BH a ranar Alhamis a yankin tsibirin Duguri na jihar Borno.

Ya ce mayakan sun yi amfani da motocin yaki masu sulke 4 da aka girkewa bindigogi a sama, da niyyar cin karfin sojojin ta hanyar zuwar musu ta bayan sansaninsu.

Wannan ya janyo musayar wuta a kokarin sojojin na dakile yunkurin mayakan. Lamarin da ya yi sanadin raunatar sojoji 4.

A cewar Aminu Iliyasu, yanzu haka sojojin da suka jikkata na jinya a asibitin soji, kuma suna samun sauki, yana mai cewa dakarun za su ci gaba da matsa lamba kan mayakan BH har sai sun murkushe su baki daya.

Kungiyar BH da ta kaddamar da hare-hare a arewa maso gabashin Nijeriya shekaru 10 da suka gabata, ta yi suna saboda manufarta ta kafa daular Islama a kasar mafi yawan al'umma dake Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China