Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Doka da ta shafi Hong Kong da Amurka ta zartas za ta sha kaye
2019-12-04 20:44:13        cri
Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya fitar da wani sharhi yau Laraba, mai taken "dokar da ta shafi Hong Kong da Amurka ta amince da ita ko shakka babu za ta sha kaye".

Sharhin ya ce, a kwanakin baya ne Amurka ta sanya hannu kan wata doka kan hakkin dan Adam da demokuradiyya na Hong Kong, duk da babbar adawar da kasar Sin ta nuna. Irin wannan abun da Amurka ta yi ya lalata bunkasuwa da kwanciyar hankali a Hong Kong, har ma ya illata moriyar Amurka da ta sauran kasashen duniya.

A cewar sharhin, bayan da gwamnatin Amurka a wannan karo ta kama aiki, akwai wasu 'yan siyasar kasar wadanda suke rike da ra'ayin cacar baki da nuna babakere da danniya, da yunkurin kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Gwamnatin Sin ta riga ta dauki matakai kan aika-aikar da Amurka ta yi, haka kuma za ta ci gaba da daukar duk wani matakin da ya wajaba bisa ga la'akari da halin da ake ciki. Sin ta kuma yi kira ga wasu 'yan siyasar Amurka, da su daina yaudara kan kasar Sin, saboda ba za su samu nasara ba, bisa burin su na hana ci gaban kasar ta hanyar amfani da batun Hong Kong.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China