Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Goyon bayan masu tada rigima a Hong Kong ba zai samu amincewar al'umma ba
2019-12-02 20:13:44        cri
Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya fitar da wani sharhi a yau Talata, mai taken "Nuna goyon-baya ga masu yunkurin tada zaune-tsaye a Hong Kong, sam ba zai samu amincewa daga al'umma ba", inda ya ce, a lokacin da ake dab da kawo karshen tashe-tashen hankali gami da farfado da zaman doka da oda a yankin Hong Kong, Amurka ta sanya hannu kan wani shirin doka kan hakkin dan Adam da demokuradiyya na Hong Kong, abun da ya samar da mafaka ga masu tada zaune-tsaye, da kawo barazana ga masu kiyaye doka da oda, tare kuma da hura wutar rikici, da kara nuna goyon-baya ga 'yan tada hatsaniya.

Wannan abun da Amurka ta yi ya shaida mummunar niyyarta ta lalata yankin Hong Kong, gami da kawo tsaiko ga ci gaban kasar Sin baki daya.

Sharhin ya kuma bada misalin cewa, kungiyar The National Endowment for Democracy ta Amurka ko kuma NED a takaice, wadda ke tallafawa 'yan hatsaniyar Hong Kong, ta rika hura wutar rikici a wasu kasashe da yankuna sama da dari a duk duniya, al'amarin da ya shaida irin aika-aikar da Amurka ta yi, wato ta nuna goyon-baya ga masu tada rigima kuma tana fakewa da kare hakkin dan Adam da demokuradiyya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China