Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dogaro kan kasar Sin shi ne tabbacin samun bunkasuwar yankin Hong Kong
2019-12-03 20:24:43        cri
Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko CMG a takaice, ya fitar da wani sharhi yau talata, mai taken "dogaro kan kasar Sin shi ne babban tabbacin samun bunkasuwa da kwanciyar hankali a yankin Hong Kong".

Sharhin ya ce, a kwanakin baya ne Amurka ta yi biris da rashin amincewar da kasar Sin ta nuna, har ta zartas da doka kan hakkin dan Adam da demokuradiyya na yankin Hong Kong, abun da ya zama shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da lalata bunkasuwa da kwanciyar hankali a Hong Kong.

Jiya Litinin, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, gwamnatin kasar ta yanke shawarar dakatar da duba rokon da jiragen yakin sojan Amurka ke gabatarwa na samun hutu a Hong Kong, da garkama takunkumi kan wasu kungiyoyin Amurka da ba na gwamnati ba, wadanda suka aikata munanan laifuka a rikicin Hong Kong, ciki hadda kungiyoyin NED da NDI da sauransu.

Sharhin ya jaddada cewa, babu tantama kasar Sin za ta dauki matakai kan abun da Amurka ta yi, kuma bai kamata a kyale irin niyya gami da matakan kasar Sin na kiyaye ikon kasa, gami da tsaro, da kuma ci gaban kasar ba.

Akwai wasu 'yan siyasar Amurka wadanda ke yunkurin hura wutar rikici a Hong Kong, abun da ko shakka babu ba zai samu amincewar al'ummar yankin ba, kuma daukacin al'ummar kasar Sin ba za su yarda ba. Makomar yankin Hong Kong na hannun al'ummar kasar Sin ciki hadda al'ummar yankin, kuma yankin zai sake samun bunkasuwa da kwanciyar hankali, bisa ga dogaro ga kasarsa ta Sin!(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China