Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da zama na farko don jin ra'ayin jama'a game da bukatar tsige shugaban Amurka
2019-11-14 11:16:45        cri
Kwamitin binciken sirri na majalisar dokokin kasar Amurka, ya gudanar da zaman sauraron ra'ayin jama'a a karon farko a jiya Laraba, biyowa bayan bukatar da 'yan majalisar daga jam'iyyar Dimokarat suka gabatar, game da tsige shugaba Donald Trump daga mukaminsa. Kwamitin dai na fatan tattara bayanai game da ko shugaban na Amurka ya keta dokar aiki, ta hanyar yin mu'amalar sirri da kasar Ukraine.

Wadanda suka bayyana gaban kwamitin sun hada da jami'in ofishin jakadancin Amurka a kasar Ukraine William Taylor, da mataimakin sakataren wajen Amurka mai lura da harkokin nahiyar Turai George Kent. Jami'an biyu dai sun riga sun yi ganawar sirri da 'yan majalissar dokokin a watan Oktoban da ya gabata, a kuma lokacin sun bayyana damuwarsu, game da mu'amalar shugaba Trump da Ukraine.

Cikin sanarwarsa ta bude zaman, shugaban kwamitin binciken Adam Schiff, wanda dan jam'iyyar Dimokarat ne da ya jima yana shan suka daga Trump, tun bayan bullar yunkurin tsige shi, ya ce burin su shi ne gano gaskiyar lamari, game da ko shugaba Trump ya yi amfani da fadar White House wajen ganawa da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, tare da tallafawa kasar da miliyoyin daloli na gudanar da ayyukan soji, domin jan hankalin Zelensky ya amince da bukatar Trump ta bincikar abokin hamayyarsa a siyasance. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China