Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar wakilan Amurka ta amince da kudurin tsige shugaban kasar
2019-11-01 11:05:46        cri

Majalisar wakilan Amurka, ta kada kuri'ar amincewa kudurin dake da nufin aiwatar da bincike kan shirin tsige shugaban kasar, Donald Trump.

Kudurin wanda kwamitin kula da ka'idoji na majalisa ya gabatar a farkon wannan mako, ya samu kuri'un amincewa 232 da na kin amincewa 196 a majalisar mai rinjayen 'yan jam'iyyar Democrat. Babu wani dan jam'iyyar Republican dai da ya amince da kudurin.

Wannan ne karon farko da majalisar ta kada kuri'a a daukacin zauren game da batun binciken tsige shugaban, tun bayan da shugabar majalisar Nancy Pelosi ta kaddamar da shirin tsigewar a karshen watan Satumba.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tweeter a jiya Alhamis, Donald Trump ya bayyana binciken tsigewar a matsayin bita da kulli mafi girma a tarihin kasar, yana mai ikirarin matakin na illa ga kasuwar hannayen jari ta kasar.

Batun binciken tsigewar ya samo asali ne bayan wani ya tsegunta tattaunawar da fadar white House da ta yi da kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa ta wayar tarho da aka yi tsakanin Donald Trump da takwaransa na Ukraine Volodymr Zelensky, a ranar 25 ga watan Yuli.

Ana zargin shugaba Trump da amfani da mukaminsa ba bisa ka'ida ba, ta hanyar amfani da taimakon soji wajen matsawa Shugaba Zelensky, ya aiwatar da bincike kan tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, wanda shi ne babban dan takarar shugabancin kasar na Jam'iyyar Democrat a zaben 2020, domin ya taimaka wajen sake zabarsa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China