Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gargadi Birtaniya ta daina tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasar Sin
2019-08-11 15:49:11        cri
Gwamnatin kasar Sin ta yi kashedi ga Birtaniya da ta guji yin katsalandan a harkokin cikin gidan Sin kuma ta daina furta kalaman batanci game da batun yankin musamman na Hong Kong, kakakin gwamnatin Sin ta bayyana hakan a jiya Asabar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying, ta bayyana cewa, a halin yanzu Hong Kong yanki ne na musamman dake karkashin ikon gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Ta kara da cewa, lokaci ya riga ya wuce da yankin ya taba zama karkashin ikon Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Kakakin ofishin ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ya ce, sakataren harkokin wajen kasar Raab, ya yi hira ta wayar tarho a ranar 9 ga watan Augasta da babbar jami'ar gudanarwar yankin Hong Kong, Carrie Lam, game da halin da ake ciki a yankin na Hong Kong.

A lokacin da aka nemi ya yi karin haske ta wayar tarho, Hua ta ce, Birtaniya ba ta da wani iko, ko 'yanci, ko kuma hakkin bibiyar al'amurran dake faruwa a yankin na Hong Kong. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China