Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta nada sabuwar wakiliyar hukumar samar da makashi mai dorewa ga kowa
2019-10-30 10:38:28        cri
Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya nada Damilola Ogunbiyi, 'yar asalin Nijeriya, a matsayin sabuwar wakiliyarsa a hukumar samar da makamashi mai dorewa ga kowa, kuma daya daga cikin shugabannin hukumar kula da makamashi ta MDD.

Ofishin yada labaran Sakatare Janar din ya ruwaito shi yana maraba da nadin Damilola Ogunbiyi a matsayin babbar jami'ar zartarwa ta hukumar samar da makamshin.

A shekarar 2011 ne aka kaddamar da hukumar samar da makamashi mai dorewa ga kowa, karkashin Sakatare Janar na Majalisar na wancan lokaci, Ban ki-Moon, da nufin cimma nasara wajen samar da makamshi na gama gari da kara ingancin makamashin da kuma inganta amfani da makamashin da ake iya sabuntawa.

Damilola Ogunbiyi, za ta maye gurbin Rachel Kyte 'yar asalin Birtaniya.

Antonio Guterres ya ce Damilola Ogunbiyi wadda yanzu ke shugabantar hukumar samar da lantarki ga yankunan karkara ta Nijeriya, na da gogewa kan harkar shugabanci tare da tarihin taimakawa yunkurin samar da makamashi a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China