Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 33 a Afrika na cikin hadarin fama yunwa saboda sauyin yanayi
2019-12-03 09:38:25        cri
Asusun bada agaji da kula da yara na Save the Children, ya yi gargadin cewa, mutane miliyan 33 daga kasashe 10 a gabashi da kudancin Afrika, na cikin hadarin fama yunwa saboda matsalolin sauyin yanayi.

Asusun ya sanar da haka ne a jiya, rana ta farko ta taron kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD.

Asusun ya ce a bana, ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa da fari da mahaukaciyar guguwa, sun yi mummunan illa ga wasu sassan gabashi da kudancin Afrika, wadanda suka jefa mutane a kalla miliyan 33 cikin yanayin bukatar abinci cikin gaggawa ko ma yanayin da ya zarce hakan.

Ya kara da cewa, la'akari da yankin na da mutane miliyan 162 masu shekaru kasa da 18, sama da yara miliyan 16 na wani mataki na bukatar abinci cikin gaggawa.

Har ila yau, asusun Save the Children ya ce wadancan matsaloli da matsanancin yanayi ya haifar, ya tilastawa miliyoyin mutane barin matsugunansu da wuraren noma, inda barin matsugunan ya jefa yara musamman masu rauni cikin yanayi na musgunawa da kamuwa da cututtukan dake da alaka da sauyin yanayi, kamar zazzabin cizon sauro.

Asusun ya yi kira ga shugabannin duniya da su dauki ingantaccen matakin rage mummunan tasirin sauyin yanayi da tabbatar da kare rayuwa da makomar yara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China