Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon firaiministan Habasha: Hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin aikin gona yana da muhimmanci
2019-11-27 13:27:10        cri
Hailemariam Desalegn, tsohon firaiministan kasar Habasha yace hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika yana da matukar muhimmanci wajen bunkasa fannin aikin gona da kawo sauye sauyen cigaban nahiyar.

A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Talata a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, Desalegn yace, fannin aikin gona na Afrika yana mayar da hankali wajen canza fasalin fannin daga noman da ake biyan bukatun gida zuwa tsarin noma na kasuwanci, wanda hakan na nufin za'a dinga samar da amfanin gonar don sayarwa a kasuwanni da kuma mayar da shi a matsayin sana'a.

Tsohon firaministan na Habasha a halin yanzu yana jagorantar wata cibiyar bunkasa aikin gona ta Afrika wato (AGRA). Ya ziyarci kasar Rwanda domin kaddamar da taron dandalin (AGRF) na 2020, wanda za'a gudanar a watan Satumbar shekara mai zuwa.

Desalegn yace, kasar Sin ta kawo sauye sauye ga tsarin aikin gona na al'ummarta cikin kankanin lokaci, wannan kyakkyawan darasi ne ga nahiyar Afrika da ya kamata su dauka domin kawar da yunwa daga nahiyar, ko da yake bai dace Afirka ta kwaikwayi Sin dari bisa dari ba..

Ya kamata kasashen Afrika su yi amfani da dabarun da kasar Sin ta yi aiki dasu bisa ga yanayin da suke ciki, in ji Desalegn.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China