Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi kira da magance matsalolin cutar kanjamau a kan rukunoni masu rauni na nahiyar Afrika
2019-12-02 09:36:45        cri
Shugaban hukumar AU, Moussa Faki Mahamata, ya yi kira da a hada hannu wajen rage matsalolin cutar kanjamau a tsakanin rukunonin mutane masu rauni a nahiyar Afrika, galibi 'yan gudun hijira da wadanda suka dawo daga gudun hijira da kuma wadanda suka rasa matsugunansu a kasashensu.

Shugaban na AU wanda shi ma ya bi sahun al'ummomin duniya wajen bikin ranar yaki da cutar Kanjamau ta duniya, don mara baya ga mutanen dake dauke da cutar a nahiyar Afrika da ma sauran sassan duniya, ya ce wadancan rukunoni na cikin hadarin kamuwa da cutar, haka ma 'yan mata masu shekaru tsakanin 15 da 19, wandanda ke ci gaba da kasancewa mafi rauni wajen kamuwa da cutar.

Moussa Faki Mahamat ya ce nahiyar Afrika ta samu nasarori a yaki da cutar kanjamau, tun bayan taron musammam da aka yi a birnin Abuja a shekarar 2001, kan cutukan kanjamau da tarin fuka da sauran cututtuka masu yaduwa, inda shugabannin duniya suka ayyana cutar kanjamau a matsayin wadda ke bukatar daukin gaggawa a nahiyar.

Da yake tsokaci kan kara damar samun magani da kulawa ga masu cutar, ciki har da wadanda ke yankunan da ake rikici, shugaban na AU ya ce ayyukan al'ummomi shi ne kan gaba wajen bada taimakon ceto rai da kwantar da hankali da kulawa da kuma kare wadanda ke tsananin bukata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China