Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci Afrika ta zuba jari a fannin ayyukan more rayuwa wanda ya ratsa kan iyakokin kasashen
2019-11-28 09:40:58        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) da hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD (UN-ECA) sun bukaci kasashen Afrika su kara zuba jari a wasu muhimman ayyukan more rayuwa da suka tsallaka kan iyakokin kasashen da nufin samar da gagarumin ci gaba da burin da ake da shi na neman dunkulewar nahiyar.

An gudanar da kiran ne a lokacin wani muhimmin taron hadakar kasuwanci na nahiyar, wanda aka shirya a matsayin wani bangare na bikin makon Afrika na bunkasa ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa na wannan shekarar wato (PIDA-2019), wanda ake gudanarwa a fadin nahiyar daga ranar 25 zuwa 29 ga watan Nuwamba.

Babban jami'in hukumar raya cigaba na kungiyar tarayyar Afrika (AUDA-NEPAD), Ibrahim Assane Mayaki, a lokacin taron ya jaddada cewa, samar da kudaden gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa wanda ya ratsa kan iyakokin kasashen zai taimaka wajen samar da bunkasuwar nahiyar Afrika.

Jami'in hukumar ta AUDA-NEPAD ya nanata cewa, hadin gwiwa tsakanin bangarorin gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen tabbatar da zuba jari cikin hanzari a muhimman ayyukan more rayuwar shiyyar.

A cewar Mayaki, daga cikin muhimman ayyukan more rayuwa da suka ratsa iyakokin kasashen sun hada da aikin gina tashar samar da lantarki a madatsar ruwa ta Ruzizi III daga kogin Ruzizi wanda ya ratsa kan iyakokin kasashen jamhuriyar Kongo (DRC), da Burundi da Rwanda, da kuma aikin shimfida bututun iskar gas daga Najeriya zuwa Algeria (Trans-Sahara Gas Pipeline).

Wasu alkaluma daga hukumar AUDA-NEPAD ya nuna cewa, sama da kashi 60 bisa 100 na ayyukan more rayuwa a Afrika gwamnati ne ke daukar nauyin gudanarwa, Mayaki ya jaddada cewa, dabarun da aka tsara na samar da kudaden gudanar da ayyukan zai taimaka wajen kara samar da hanyoyin tattara kudaden gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa a nahiyar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China