Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hong Kong zai zama Hong Kong na kasar Sin na dindindin!
2019-11-27 14:42:54        cri

Bayan dawo da yankin Hong Kong kasar Sin a shekarar 1997, cikin shekaru 22 da suka gabata, yankin Hong Kong ya sami 'yancin kai, kuma ya samu babban ci gaba bisa jagorancin kwamitin tsakiyar gwamnatin kasar Sin. Kana, ya more kyawawan sakamako da dama da babban yankin kasar Sin ya samu bayan da ta fara aiwatar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, inda ya kuma dauki nauyin farfadowar kasar Sin.

Duba da babban ci gaban da kasar Sin ta samu, 'yan siyasa na kasar Amurka da wasu yammacin kasashen duniya sun fara neman jan kasar Sin baya da muggan matakai, kamar yanzu suna neman sanya yankin Hong Kong cikin rashin kwanciyar hankali. Ko shakka babu, ba za su ci nasara ba. Yankin Hong Kong wani bangare ne na kasar Sin, duk abun da ke faruwa a wurin ba zai canja matsayinsa ba. Kasar Sin ba za ta yi hakuri ko kadan ba, kan wadanda suke neman bata tsarin "kasa daya mai tsarin mulki biyu". (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China