Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaiwa jirgin saman fasinjan Kamaru hari a filin jirgin saman Bamenda
2019-12-02 10:51:53        cri

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa, an kaiwa wani jirgin saman fasinjan kasar hari ranar Lahadi da safe a filin tashi da saukar jiragen saman Bamenda, dake yankin da ake magana da Turancin Ingilishi na kasar mai fama da tashin hankali.

Wani jami'in soja da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wasu 'yan bindiga ne suka bude wa jirgin saman na Camair-Co, mallakar gwamnatin kasar wuta, a lokacin da yake kokarin sauka. Sai dai babu wanda ya ji rauni a sanadiyar harin, amma harsasai sun bugi fuffuken jirgin na hagu suka kuma shiga cikin dakin matukin jirgin. Koda yake nan da nan jami'an tsaro sun dakile harin.

Harin na ranar Lahadi, shi ne na farko da aka kaiwa wani jirgin saman fasinja, tun lokacin da tashin hankali ya barke a yankin arewa maso gabashi da kudu maso yammacin kasar da ake magana da turancin Ingilishi a shekarar 2017.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China