Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru: Ana fatan tattaunawar kasa za ta kawo karshen bukatar 'yan aware
2019-10-01 14:57:00        cri
Firaministan kasar Kamaru Joseph Dion Ngute, ya ce gwamnati na daukar aikin dawo da managarcin yanayin zaman lafiya da tsaro, a yankunan Kamaru masu fama da tashe tashen hankula da matukar muhimmanci.

Mr. Ngute ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin da yake bude taron tattaunawa na kasa, wanda ake fatan zai kawo karshen rigingimu dake addabar wadannan yankuna biyu, dake magana da turancin Ingilishi a tsawon kusan shekaru 3.

Firaministan na Kamaru, ya ce taron wanda za a kammala a ranar Juma'a mai zuwa, zai mayar da hankali ga warware matsaloli 8 dake da nasaba da amfani da yaruka biyu, da harkar raya Ilimi, da fannin shari'a, da rarraba iko, da sake ginawa, da raya yankunan da tashe tashen hankula suka daidaita. Sauran sun hada da mayar da 'yan gudun hijira gida, da sake shigar da masu dauke da makamai da suka amince su kwance damara cikin al'umma, da kuma inganta gudummawar 'yan yankin mazauna kasashen ketare.

Yayin bikin bude shawarwarin, daya daga tsoffin manyan 'yan awaren da ya halarci zaman ya rera taken kasar, a matsayin wata alama ta burin bangarensu, na rungumar zaman lafiya, da amincewa da dunkulewar kasar.

Wasu daga jagororin 'yan awaren dake zaune a cikin kasar dai sun ki amsa gayyatar halartar taron, suna masu zargin cewa, ba a shirya shi da zuciya daya ba, kuma ba a gayyaci dukkanin sassa ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China