Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU da abokan huldarta sun yaba da taron tattauna batutuwan kasa da aka gudanar a Kamaru
2019-11-30 16:27:53        cri
Tarayyar Afrika AU da abokan huldarta, sun yaba da matakan da shugaban Kamaru, Paul Biya, ya dauka a baya bayan nan, da nufin rage dumamar yanayin siyasa a yankin yammacin kasar dake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi.

Wannan na zuwa ne bayan kammala taron da ya gudana jiya Juma'a, tsakanin shugban hukumar AU, Moussa Faki Mahamat da shugaban Kamaru Paul Biya, wanda ya kuma samu halartar Sakatare Janar na kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransanci ta OIF, Louise Mushikikwabo da takwararsa ta kungiyar kasashe rainon Ingila, Patricia Scotland, game da yanayin siyasa da ake ciki a Kamaru.

Tarayyar Afrika da shugabannin kungiyoyin OIF da na kasashe rainon Ingila, sun yi maraba da babban taron tattauna batutuwan kasa, wanda ya bude sabon babi tare da bada shawarar rarraba iko ga matakan gwamnati daban daban da bada matsayi na musamman ga yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammcin kasar da nazarin tsarukan ilimi da shari'a, ciki har da matakan da shugaba Biya ya dauka na rage dumamar yanayin siyasa da sauransu.

Jami'an 3 sun kuma jaddada cewa tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa ta samar da mafita ga yanayin da kasar ke ciki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China